A Fada A Cika: Tattaunawa kan matsalolin ilimin piramare a arewacin Najeriya
HTML-код
- Опубликовано: 7 сен 2024
- Wannan shirin na A Fada A Cika tare da talafin Gidauniyar McArthur ya tattauna kan batun matsalolin dake addabar ilimin pirmare a Najeriya, musamman ma yankin arewacin kasar.
Kwamishinonin ilimi na jihohin Kano da Katsina da Jigawa ne suka kasance manyan baki. Sannan akwai kuma sauran masu ruwa da tsaki da suka kasance cikin tattaunawar.
Daga cikin wadanda suka halarta har da wasu daliban makarantun piramare da suka yi magana kan matsalolin da suke fuskanta a makarantunsu.
Gaskiya wannan matsalar akwaita sosai Kuma gyara bazai yuwuba kwata kwata tunda wadanda keda alhakin gyaran sukeda makarantun kudi Nigeria sai a hankali Allah ya kawo mafita
Allah ya kawo mana dauki. Ameen
Thanks 👍
Wannan haka yake duk matsalolin kusan iri daya ne a makarantun gwamnati a arewacin Nigeria, ni malama ce a wata makarantar gwamnati a karamar hukumar Toro a jahar Bauchi. Makarantana akwai tun daga nursery har baban sakandere amma babu aji guda daya a makarantar wanda ruwa baya zuba balle maganan wajen zama wannan kan ba a maganan shi. Allah dai ya kawo mana dauki amma makarantun gwamnati tana dab da shafewa gaba daya a arewa in ba wani ikon Allah ba
Muna godiya malama da wannan karin bayani
Kai najeriya kasa ta😮😮😅