Sarki Sanusi ya yi tsokaci kan darajar Naira

Поделиться
HTML-код
  • Опубликовано: 10 сен 2024
  • Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi 11, ya bayyana gamsuwarsa da kamun ludayin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
    A wata hira ta musamman da BBC a wata ziyara da ya kai Africa ta Kudu, Muhammadu Sanusi na biyu ya ce, gwamnatin Shugaba Buhari ta yi kokari wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki da kungiyar Boko Haram, kuma dukkanin wadanann abubuwa ne da za su taimakawa tattalin arzikin kasa.
    Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce a matsayinsa na mai goyan bayan gwamnatin Muhammadu Buhari ya zama wajibi ya ba ta shawara ta duba manufarta a kan darajar Naira.

Комментарии • 20