Duniyar Nan | Kashi Na 5 | AREWA24

Поделиться
HTML-код
  • Опубликовано: 6 фев 2025
  • STORY A
    DUNIYAR NAN
    Labarin ya fara da Alhaji Lawal, magidanci, dan kasuwa mai arziki, wanda ke da burin shiga siyasa. Alhaji Lawal na da mata biyu: uwargidansa mai yara uku (mazan biyu da mace ɗaya) da amaryarsa wacce ke da ɗa kaɗai. Duk da nasararsa a kasuwanci, Alhaji Lawal mutum ne azzalumi wanda ke tauye hakkokin ma’aikatansa da waɗanda suka kasa shi. Har ma ya dogara da wani boka don samun nasara a duk harkokinsa.
    A yayin da yake kokarin korar babban ma’aikatansa, Alhaji Auta, saboda ya faɗi gaskiya, hakan ya jawo masa matsaloli. Sai dai Allah ya albarkaci Alhaji Auta, wanda daga ƙarshe ya gina kansa kuma ya zama abun kishi ga Alhaji Lawal. Wannan hassada ce ta ƙara tunzura Alhaji Lawal.
    Amaryar Alhaji Lawal mace ce mai kyau da iya kwalliya wacce ta mallake shi ta kuma lalata dangantakarsa da uwargidansa. Da taimakon aminiyarta, ta fara zuwa wajen boka, inda ta saka ƙiyayya cikin zuciyar Alhaji Lawal ga uwargidansa har ya koreta daga gida. Sai dai daga baya ta dawo zaman kishi da ɗiyar uwargidan, Mansura, wacce bata goyi bayan mugunta ba.
    Amaryar ta kuma kamu da soyayya da direban da ke kai ɗanta makaranta. Haka suka fara cin amanar Alhaji Lawal ba tare da ya gane ba. A ƙarshe, aminiyarta ta janye Alhaji Lawal zuwa gareta, suka fara shirye-shiryen aure, lamarin da ya tayar da hankali a gidan.
    Mansura, ɗiyar Alhaji Lawal, tana matashiyar da bata tsoron kowa. A jami’a, ta kasance marar sassauci, amma soyayya da wani matashi ajinsu ya natsar da ita. Ta haɗa kai da yayyenta domin ganin sun kwatar wa mahaifiyarsu ‘yanci. Duk da haka, mahaifiyarsu ta ki dawowa gidan saboda tsoron Alhaji Lawal. A ƙarshe, hakuri da juriyarta suka zama mata jari, yayin da gaskiya ta yi halinta.

Комментарии •

  • @BassiruHaussa
    @BassiruHaussa 5 дней назад

    Good 🎉🎉🎉🎉❤❤❤

  • @farydajalo9574
    @farydajalo9574 5 дней назад

    Gaskiya Arewa24 Baku kyauta manaba dakuka cire adama a dadin kowa Don Allah kudawa da ita

  • @AbdourahamaneSamo-k9q
    @AbdourahamaneSamo-k9q 5 дней назад

    ❤❤❤

  • @NaziraArma
    @NaziraArma 7 дней назад +2

    ❤❤❤❤❤❤🎉🎉😢