A rana irin ta yau: Fabrairu 1, 2013 Aka tuhumi Faruku Lawan da rashawar $500,000

Поделиться
HTML-код
  • Опубликовано: 16 сен 2024
  • A rana irin ta yau: 1 ga Fabrairu 2013 Aka tuhumi Farouk Lawan da rashawar $500,000.
    An tuhumi shugaban kwamitin Majalisar tarayya mai binciken badaƙalar kuɗaɗen tallafin mai kuma wakilin mazabar Ɓagwai da Shanono dake jihar Kano Honorabul Faruk Lawan da karɓar cin hancin Dal dubu 500 daga babban ɗan kasuwa Mista Femi Otedola.
    A watan Janairun 2012 ne Faruk Lawan ya jagoranci kwamitin bincike kan yadda ake kashe kuɗaɗen tallafin mai na gwamnati.
    An kafa kwamitin ne a lokacin da gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta janye tallafin man fetur abin da ya jawo ƙarin farashin man, lamarin da ya haifar da zanga-zangar da aka yi wa laƙabi da "Occupy Nigeria".
    Rahoton da kwamitin ya fitar a watan Afrilun 2012 ya gano cewa kamfanonin dillancin man fetur sun handame wa gwamnatin Najeriya fiye da Dala biliyan 6 da dubu 800.
    Sai dai shugaban ɗaya daga cikin kamfanonin da ake zargi da hannu a badaƙalar wato Femi Otedola ya yi zargin cewa, ɗan majalisa, Farouk Lawan ya karɓi cin hanci domin fitar da kamfaninsa , Zenox daga cikin jerin kamafonin da kwamitin majalisar wakilan ya bincika.
    Rahotanni a lokacin sun ce da fari kuɗaɗen da gwamnati ke bin kamfanin ya kai dala miliyan ɗaya, amma daga baya sai aka cire shi daga cikin rahoton.
    Kuma sai ga bidiyo ya bayyana lokacin da Faruk Lawan ke karɓar kuɗin ‘toshiyar bakin”.
    Bidiyon mai tsawon minti biyu ya yaɗu sosai a shafukan intanet a wancan lokacin.
    Sai dai tun a sannan Farouk Lawan ke kare kansa da cewa ya karɓi kuɗaɗen ne ba da niyyar rufa wa kamfanin Zenox asiri ba, sai don ya ga iya gudun ruwansu tare da miƙa lamarin ga Hukumar Yaƙi Da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati, EFCC.
    Amma Otedola ya ce ya kai ƙorafi ne gaban Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya DSS cewa Lawan ya buƙaci ya ba shi cin hancin dala miliyan uku don rufa wa kamfaninsa asiri.
    Sai hukumar DSS ta tura jami'anta suka dasa kyamara a inda za a gana da Lawan sannan aka miƙa masa ƙunshin kuɗin.
    Lawan ya karɓa ya sanya a aljihu sannan ya riƙe ɗaya ƙunshin a hannu kamar yadda aka gani a bidiyon.
    A rana irin ta ya kuma u 1 ga Fabrairun 2013 aka gurfanar da Farouk Lawan gaban kotun tarayya dake Abuaja bisa tuhumar karbar cin hancin dala dubu 500.
    Sai dai ya musanta zarge-zargen da ake yi masa wanda hakan yasa kotu ta tasa keyarsa zuwa gidan yari kafin bayar da belin sa a wancan lokaci.
    A watan Yunin shekarar 2021 ne kuma kotun ta daure Farouk Lawan, shekaru 7 a gida yari.
    Sai dai ya ɗaukaka ƙara inda kotun ta sassauta masa daga shekaru 7 zuwa biyar.
    Nan ma bai tsaya ba inda ya garzaya kotun koli.
    A ranar 26 ga Janairun 2024 da muke ciki ne kotun kolin ta sake tabbatar da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke masa.
    Farouk Lawan ɗan asalin jihar Kano ne.
    An zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Ɓagwai/Shanono daga jihar Kano tun a shekarar 1999.
    Sannan ya kasance a majalisa har sau huɗu wato tun daga zaɓukan 1999 har zuwa na 2015 ƙarƙashin jam'iyyar PDP.
    Sai dai ya sha kaye a zaɓen 2015, lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasara.
    Farouk Lawan ɗan majalisa ne mai matuƙar ƙarfin faɗa a ji a majalisar dokoki a wancan lokacin.
    Ya taɓa zama shugaban Kwamitin Kuɗi na Majalisar Wakilai a lokacin da Aminu Bello Masari ke jagorantar ta.
    Shi ne ya jagoranci wata gamayya ta ƴan majalisa wato Integrity Group, masu son tabbatar da gaskiya da suka yi adawa da Shugabar Majalisa Patricia Etteh a lokacin da ta shiga wata badaƙalar cin hanci a 2007, wadda har ta yi sanadiyyar yin murabusa ɗinta.
    A dalilin wannan lamari ne har aka ba shi laƙabin Mr Integrity a majalisar.

Комментарии •