A rana irin ta yau: Janairu 24, 1983 Ɓarayin gwamnati suka ƙone ginin da yafi tsawo a Lagos
HTML-код
- Опубликовано: 2 ноя 2024
- A ranar 24 ga Janairun 1983 aka ƙone ginin da yafi tsawo a Lagos saboda badaƙalar Dala miliyan 100
A jamhuriya ta Biyu, ma’ikatan gwamnatin Najeriya sun yi ƙaurin suna wurin ƙone ofisoshinsu duk lokacin da ake bincike kan badaƙalar kuɗi.
A 1980, gobara ta tashi a sahen kuɗi na ma’aikatar ilimi bayan da ake nemi wasu kuɗi aka rasa.
A shekarar ne kuma aka ƙone ma’aikatar kuɗi ta jihar Imo.
A jihar Gongola ma, lokacin da aka ɓatar da Dala Miliyan uku a hukumar bunƙasa aikin noma sai aka cinnawa ginin wuta domin kaucewa bincike.
A 1981, hedikwatar ma’aikatar hulɗa da ƙasashen waje dake Republic Building mai hawa 11 ta ƙone ƙurmus bayan da wuta ta tashi a ofishin hada-hadar kuɗi na ma’aikatar.
A nan kuma, Dala miliyan guda ce aka wawure.
A Disamban 1982 ma an kwata, inda aka sace dala miliyan 21 a hukumar raya birnin tarayya Abuja.
A na kafa kwamitin bincike sai gini ya kama da wuta.
Haka ma abin ya kasance a gidan talabijin na jihar Anambra, wato ABC Enugu.
Daga nan kuma sai Sashen kiran waya zuwa ƙasashen waje na Najeriya wato N.E.T inda aka tuhumi shugabannin hukumar da sace fiy da dala milyan 100.
Wannan ta jawo aka sallami Manajan Daraktan hukumar tare da wasu daraktoci takwas domin samun damar bincike.
Ginin hukumar mai suna NECOM House yana da hawa 32 kuma lokacin da aka buɗe shi a 1979 shi yafi kowanne gini tsaho a Afirka ta yamma.
Don haka aka girke jami’an ƴan kwan-kwana domin bai wa ginin kariya daga gobara.
Sai dai bayan kwanaki kaɗan sai aka janye ƴan kwana-kwanar.
Mahukuntan N.E.T suka roƙi hukumar kashe gobara ta dawo da su amma ba ta amince ba.
Sai daga biya ne bincike ya nuna cewa ashe cin hancin dala dubu 75 aka bayar domin su kauce su bada wuri.
A rana irin ta yau kuma, wato 24 ga Janairun 1983 sai wuta ta kama ganga-ganga a hawa na shida kuma kafin ƙarfe ɗayan rana ta kai hawa na 17.
Gobarar ta kashe mutane biyu ciki har da tsohon editan jaridar New Nigerian Malam Aminu Abdullahi.
Sannan kuma ta jikkata fiye da mutane 60 a ƙididdigar hukuma.
Har sai sojin sama suka je da helikwafta suka yi ta ceton mutane daga saman ginin.
Amma wasu da gobarar ta rutsa da su sai ta taga suka riƙa dira suna karyewa.
Wannan gobara ta gigita mazauna birnin Lagos.
Da yake ginin ba shi da nisa da Majalisun Dokokin Tarayya sai da shugaban majalisar dattawa Sanata Joseph Wayas da na Majalisar Tarayya Edwin Ume-Ezeoke suka ja tawaga zuwa wurin domin ganin yadda ake ƙoƙarin kashe gobarar.
Shi ma Ministan sadarwa Audu Ogbeh ya yi ta kai gwauro ya kai mari har aka kashe wutar.
A jawabinsa ga manema labarai, ya yi zargin cewa da gangan aka cinna wutar saboda daƙile yunƙirin da yake yi na tsaftace ma’aikatar daga cin rashawa.
Ya kuma ce wannan gobarar ta sa ba za a iya kiran ƙasashen waje a tarho daga Najeriya ba saboda na’urorin aikin sun ƙare.
Amma an ci sa’a an kammala aikin sabon ofishin hukumar dake Kaduna don haka duk wanda zai kira wata lambayar tarho daga Najeriya zuwa ƙasashen waje sai ya yi amfani da lambar Kaduna maimakon Lagos.
Daga nan kuma ya bada tabbacin gudanar da bincike domin hukunta waɗanda suka aikta wannan ta’asa.
Washegari kuma sai ɗalibai daga Jami’ar Lagos da Kwalejin Fasaha ta Yaba suka gudnar da zanga-zangar neman gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin gaggawa na magance ƙone ma’aikatu da zarar an tafka badaƙala.
Daliban sun afka cikin ginin Majalisar Dokoki ta Tarayya inda suka hana zaman Majalisar Dattawa da ta Tarayya.
A cikin arangamar ne suka zane Sanata Tony Anyanwu na jam’iyyar NPP daga jihar Imo.
Haka kuma sun farfasa motar Dr Muhammadu Junaidu na jihar Kano jagoran jam’iyyar PRP a Majalisar Wakilai.
Sai dai ƴan sanda suka yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye amma abin ya ci tura.
Daga bisani babban sufeton ƴansanda IG Sunday Adewusi da shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Olusola Saraki suka basu baki sannan ɗaliban suka janye zuwa makarantunsu.
Bayan da aka kammala bincike cikin watan Fabrairu, an samu manyan ma’aikatan NET 21 da hannu cikin tada gobarar.
Take aka sallame su, aka gurfanar da su gaban kotu.
Ita kuma ta yanke musu hukuncin zaman kurkuku.
Shi kuma ginin Gwamnatin Tarayya ta gyara shi an ci gaba da amfani da shi.
Amma a watan Disamban 2015 gobara ta sake tashi a ginin.
Sai dai a wannan karon daga hawa na 32 ne kuma an yi nasarar kashe wutar ba tare da ta yi ɓarna mai yawa ba.
Ashe Andade anayi to allah Mana cikawa da imabi
Allah ya tsare mu zuwa lahira da haƙƙin mutane
Hmm Nigeria kamarsu ta gado, duk da matsalolin da suke cikinta muna qlfahari da ita.