'Ni mafarauci ne kafin na fara yin fim'

Поделиться
HTML-код
  • Опубликовано: 25 дек 2024
  • Daga bakin mai wani shiri na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah.
    A wannan kashi na uku, fitaccen mai bayar da umarni a fina-finan Hausa na Najeriya Falalu Dorayi ne, ya amsa tambayoyi da za su sa ku dariya ciki har da batun cewa shi mafarauci ne kafin ya fara fim.
    Daga bakin mai ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah.
    A wannan kashi na biyar, fitaccen mawaki kuma dan wasan fina-finan Hausa na Kannywood, Ado Gwanja ne ya amsa tambayoyin da za su sa ku dariya ciki har da cewa "zai yi wuya ya kara aure kasancewar shi 'kan-ta-ce ne.''
    Ado Gwanja ya kuma shaida wa BBC irin matar da yake so "ba doguwa ba, ba gajeriya ba kuma ba siririya ba ba mai kiba ba."
    Dangane da sana'ar gidansu da ya gada, ya ce "ba don waka ba da watakila yanzu shayi nake sayarwa", saboda a cewarsa mahaifinsa ne mai shayin Sarkin Kano.
    "Idan Sarkin kano zai sha shayi sai ya turo wurin mahaifina."
    Website: www.bbc.com/hausa
    Facebook: / bbchausa
    Instagram: / bbchausa
    Twitter: / bbchausa

Комментарии •