Shirin DW na Rana 07.12.2023

Поделиться
HTML-код
  • Опубликовано: 20 окт 2024
  • Barkanmu da wannan lokaci. Shirinmu na rana da Abdulkarim Muhammad Abdulkarim zai gabatar, ya yi muku tanadin wadannan rahotanni:
    Majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta hanzarta tsamo wadanda ke da hannu cinin harin bama-bamai da sojoji suka yi kuskuren kaiwa kan masu Maulidi a Kaduna domin hukunta su.
    Daga Kano kuma martini ake mayarwa a game da matakin wata babbar kotu a Abuja da ta rufe dukkanin asusun gwamjnatin jihar, har sai ta biga diyyar wadanda aka rusa wa gine-gine.
    A Nijar kuwa sakamakon daminar bana ke nuna alamun barazanar karancin abinci kwarai a garuruwa da dama na jihar Tahoua, inda alkaluma suka tabbatar da cewa sama da garuruwa 600 ke cikin matukar bukata a yanzu.
    Hukumomin lafiya da na noma a kasar Malawi, sun bukaci da a tsaurara bincike a kan bullar annobar cutar dabbobi ta anthrax da ke shafar 'dan adam kai tsaye.

Комментарии • 1

  • @MammanLawwali
    @MammanLawwali 10 месяцев назад

    👍👍🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇧🇫🇧🇫🇧🇫🇲🇱🇲🇱🇲🇱