ABUBUWAN BUQATA WAJEN FARA KASUWANCIN FITAR DA KAYAN ABINCI KASASHEN WAJE HANYOYIN GUDANARWA.

Поделиться
HTML-код
  • Опубликовано: 12 сен 2024
  • Abu Na farko da za a buqata wajen wannan kasuwancin shine mutum ya san me zai sayar, kamar yadda nayi bayani a Baya, Ana fitar da kayan Abinci Iri iri qasashen waje musamman don mutanen Najeriya da suke zaune a wadannan kasashen, kadan daga cikin Irin abubuwan da za
    a iya fita da su,akwai zobo, Agushi, Goro, busasshen kifi, Agada Doya, manja, crayfish, zogale, garin Doya, dodon kodi, Namijin goro, ugu, shuwaka, ogbono, kubewa, Da dai abubuwa da dama.yana da Kyau mutum ya san me zai zaba a cikin wadannan da zai dinga fitarwa zuwa kasar wajen.
    Abu Na biyu shine Neman mutanen da za ka sayarwa da kayan, A Kowanne Irin kasuwanci yana da Kyau ka fara Samun masu saye kafin ka nemi abinda za ka Sayar din, ba wai ka aje kayan sayarwar ba kuma ba ka da masu saya, idan kuna biye da ni, a gaba zan nuna hanyoyi Daban Daban da za a nemi wadanda za a sayarwa da kayan a kasashen wajen.
    Na uku shine Rajista ta kasuwanci, ma'ana Business Registration kuma ana so ta zama limited liability, kun san Rajistar kasuwanci Iri biyu ce da Akwai Register ta business Name, Akwai kuma Limited liability.
    Abu Na 4,shine Export license ma'ana takardar sahalewar gwamnati na fita da kayan zuwa kasashen waje.
    Anan Wataqila kuce abin mai wahala ne, A a sam ba shi da wahala ya danganta da yadda ka ke son tsara kasuwancin naka.
    Idan ya Kasance kana son ka dinga fitar da kaya da yawa kamr ace idan zobo za ka fitar da shi, citta ko gawayi ko ma Kowanne Irin abu ne, za ka fitar kmar container Guda ko fiye da haka, To wannan lallai kana buqatar Rajista Ta business, kmr yadda na fada a Baya limited liability, idan kuma ya Kasance kayan da ka sarrafa da kanka ne ko a kamfaninka bayan Rajista ta business kana buqatar Nafdac Registration, da kuma fda registration idan ka yan da za ka fitar za ka kaisu US A ne, amma idan ba USA za ka kai su ba ba ka buqatar Fda.
    Na san kun san Hukumar Nafdac a Najeriya, Hukuma ce da take kula da tsabta da kuma ingancin abinci wadda Duk Wani abu da za ka sarrafa wanda ya danganci ci Wani lokacin ma har da shafawa Akwai buqatar su duba su tantance ingancinsa, haka FDA take a Amurka aikinsu Iri daya ne da Nafdac sai dai Dan banbanci kadan, in da A Najeriya Kowanne abu da kake sarrafa wa sai ka samar masa Lambar sa Daban, a amurka idan ka samu Lamba daya ta wadatar ga dukkan Kayayyakin da kake sarrafa wa. Wannan kenan
    Bari mu tsallaka mu ga Manyan hanyoyi Guda 3 da ake amfani da su wajen wannan kasuwancin.
    1Hanya ta farko itace wadda idan mutum ya zabi Shiga da kayan da yawa kmr yadda nayi bayani a Baya zai yi wasu registrations, sannan yana buqatar website mai Kyau in da mutane za su duba su ga Irin abubuwan da yake samarwa da yadda zai aika musu da shi. Kmr yadda na fada a Baya wannan Hanyar tana buqatar Babban jari.
    2 Hanya ta biyu shine ta Hanyar Amfani da E commerce website (wanda shima muna koyar da mutane yadda za su bude e commerce din da kan su,muna kuma karbar aikin mu yiwa mutane in ba da kan su suke so suyi ba)Anan mutum zai bude kantinsa a yanar gizo ya Saka kayan da yake sayarwa bayanansu, da kudadensu,kamar jumi'a ko Amazon,anan website din masu saya za su saya su biya har da kudin shipping, su bada address din su kai kuma ka tura musu da kaya, wannan Hanyar tana da sauqi, Duk da tana buqatar kudi amma bai kai kmr na farko din ba. Za ku ma ka iya saka kayan naka a website din Amazon idan ka cika qa'idojinsu, ka'idojin sune, Rajistar Kasuwanci, Nafdac da kuma fda.
    3-Hanya ta uku ita ce ta Hanyar Amfani da kafafen sada zumunta kmar facebook da instagram, Abinda kawai mutum yake nema anan shine Account na business na facebook da instagram in da zai dinga tallata kayansa, wannan Hanyar tafi kowacce sauqi, mutum na iya farawa ko ba kudi ko kuma da kudi qalilan. A darasi Na gaba zan nuna muku yadda za ku samu masu sayen Kayayyakin a kasar waje. Bissalam.
    Domin tuntubaapi.whatsapp.c...

Комментарии •